Kane ya cimma yarjejeniya da Bayern Munich

0
267

Dan gaban Ingila Harry Kane ya cimma yarjejeniya da Bayern Munich inda zai bar Tottenham ya koma can a kann yarjejeniyar shekara hudu.

Kocin kungiyar Bayern Munich Thomas Tuchel ya sanya Kane a matsayin babban wanda ya sa a gaba wanda idan har bai koma kungiyar ta sa ba to zai iya shiga wani yanayi.

Tottenham na duba yiwuwar daukar dan gaban Chelsea Romelu Lukaku, mai shekara 30, idan har Kane ya koma Bayern.

Dan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24, ya sake nanata wa Paris St-Germain cewa ba zai bar kungiyar a kakar bana ba har sai kwantiraginsa ta kare.

Liverpool na kan gaba wajen daukar dan tsakiyar Brighton Moises Caicedo,inda ta zarta Chelsea, sannan kuma zata biya kudin da bata taba biya ba a tarihi a kan dan wasan dan kasar Ecuador.

Ita kuwa Chelsea, na sha’awar dan tsakiyar Italiya Marco Verratti, wanda baya cikin sabbin wadanda kocin PSG ke son dauka.

Kocin Napoli Aurelio De Laurentiis, ya ce dan gaban Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24 zai ci gaba zama da kungiyar ta Serie A har zuwa kaka mai zuwa.

Ita kuwa Everton Leeds ce ta shaida mata cewa dan gaban Italiya Wilfried Gnonto, mai shekara 19, bana sayarwa ba ne, inda yanzu ta ke dab da sayen dan gaban Portugal Youssef Chermiti daga Sporting Lisbon.

West Ham kuwa zaman jiran matakin da dan bayan Ingila Harry Maguire zai yanke ta ke a kan komawa kungiyar bayan cimma yarjejeniyar fam miliyan 30 a kan dan wasan tare da Manchester United .

An shaida wa Manchester City cewa sai ta biya fam miliyan 80 idan tana son daukar dan tsakiyar Brazil Lucas Paqueta,daga West Ham.

Real Madrid na duba yiwuwar daukar mai tsaron ragar Spaniya David de Gea, wanda ya bar Manchester United bayan kwantiraginsa ta kare, bayan da mai tsaron ragarsu Thibaut Courtois, ya ji rauni a gwiwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here