An dakatar da aikin gina dam na samar da lantarki a Nijar saboda takunkumi

0
306

Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar China Gezhouba Group ya dakatar da aikin gina aikin samar da wutar lantarki na Kandadji a Nijar wanda ya ce yawancin kudadensa an dakatar da su saboda takunkumin da aka saka wa kasar a halin yanzu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Agusta, kamfanin ya ce zai dakatar da ayyukansa tare da sallamar ma’aikatanta, yana mai cewa za su sake tura ma’aikata wurin da suke aikin kwangilar, amma sai sun tabbatar da kudi ya shigo musu.

Dam din, bayan kammala shi, ana sa ran zai bunkasa gibin tattalin arzikin kasar da kashi 50%.

Al’ummar Nijar sun fuskanci karancin wutar lantarki inda mutane miliyan 4.3 kacal ke samun makamashi yayin da kashi 90% na al’ummarta ke amfani da itace a matsayin gurbin makamashin na zamani.

Takunkumin baya-bayan nan da kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirka ECOWAS ta sanya ya gurgunta tattalin arzikin Nijar inda masu ba da taimako da sauran kungiyoyin kasa da kasa suka yanke alakarsu da ita.

Ana kuma sa ran cewa madatsar ruwan za ta taimaka wajen shawo kan kogin Neja wanda zai sa a yi noman rani.

Tun a shekarun 1970 ake tattaunawa kan yadda za a inganta wannan aiki na madatsar ruwan.

Ana sa ran kammala aikin madatsar ruwan a watan Maris din shekarar 2026, kuma za a samar da wutar lantarki sama da 130MW da za a rarraba a ciki da kuma kasashen makwabta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here