Shawarar da shugabar WTO ta ba wa Tinubu kan tsadar rayuwa a Nijeriya

0
284

Darakta Janar na hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonlo-Iweala ta ce Nijeriya na bukatar bullo da shirye-shiryen da za su taimaka wa al’umma wajen samar da ayyukan yi ga matasa da mata.

Okonlo-Iweala ta bayyana hakan ne da take yi wa manema labarai jawabi a fadar shugaban kasa bayan ganawarta da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata, ta ce bullo da shirye-shirye na al’ummar kasa zai magance wasu matsalolin da ke addabar ‘yan Nijeriya a halin yanzu.

“Mun ga shugaban kasa, kuma mun tattauna kan yadda za mu tallafa wa ‘yan Najeriya a wannan lokaci na bukata. Duk mun san cewa ‘yan Nijeriya na cikin matsanancin halin, kowa yana kokawa. Hakan ne ma ya sa na kawo wannan ziyara da kaina. Wannan ba aikin WTO ba ne a hukumance, amma mun sami damar tattaunawa da shugaban kasa kan irin shirye-shiryen da za a iya yi don tabbatar da cewa ana rage radadin da’yan Nijeriya ke sha.

“Mun gudanar da tattaunawa mai matukar muhimmanci kan kokarin bullo da tsare-tsare da za su taimaka wa al’umma wajen samar da ayyukan yi ga matasa, kuma tallafa wa mata da kananan yara, wadanda za su rage wasu wahalhalun da ake fama da su a cikin kasa.

“Mun yi magana na tsawon lokaci, muna bukatar samun damar saka hannun jari da Nijeriya za ta iya dogaro da kanta, ciki har da habaka masana’antar sarrafa magunguna. Mun kuma yi magana kan irin tallafin da hukumar kasuwanci ta duniya za ta iya kawowa.

“Mun yi aiki a Nijeriya tare da mata, musamman wadanda suka mallaki kanana da matsakaitan masana’antu don kokarin taimaka musu wajen inganta kayayyakinsu ta fannin noma, masaku da sauran fannoni domin su samu damar sayar da su da daraja a kasashen duniya.

“Muna kokarin taimaka musu ta fannin fasahar zamani, domin mu horar da matan Nijeriya da masu kananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu wajen kara habaka kasuwancinsu da samar da ayyukan yi.

“Abin da muka tattauna da mai girma shugaban kasa kenan a matsayina ta darakta janar ta kungiyar kasuwanci ta duniya, za mu yi kokarin iya bakin  kokarinmu don tallafa wa ‘yan Nijeriya a wannan lokaci,” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here