Gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaddamar da babban gangamin duba marasa lafiya kyauta, wanda zai magance wasu cututtuka da suke addabar al’umma.
Sashe na farko na wannan shiri an fara shi ne da haɗin gwiwa da ofishin matar gwamnan jihar, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, wanda zai taimakawa mutanen da ke fama da cutar yanar ido (cataract), cutar gwaiwa (groin swellings), cutar yoyon fitsari (VVF) da kuma ilimin yadda za su kiwata lafiyarsu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce wannan gangami na kula da kiwon lafiya kyauta an fara shi ne ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka samu nasarar yi wa mutum 81 aikin ido, da kuma yi wa mutum 49 aikin cutar gwaiwa.
Ya ƙara da cewa, wannan babban gangami na kiwon lafiya an tsara duk wata zai yi aiki ga masu cutar gwaiwa mutum 1, 000, za a kuma yi wa mata 200 masu fama da yoyon fitsairi aiki, haka nan za a yi aiki ga mutum 1, 000 masu fama da ciwon ido.
Sanarwar ta ce: “Gwamnatin Zamfara ta kafa kwamiti ne na ƙwararru waɗanda suka yi bincike suka tsamo nau’ikan cututtukan da ke addabar mutane.
“Binciken kwamitin ne ya tabbatar da cewa, mutane sun fi buƙatar aiki kyauta a cututtuka irinsu yanar ido, cutar gwaiwa, cutar yoyon fitsari da ilimin yadda za su kiwata lafiyarsu.
“Wannan shi ne karo na farko a Jihar Zamfara da gwamnati take yin gangami don kula da kiwon lafiyar jama’a masu fama da manyan cututtuka.
“Wannan gangami ya bayar da dama ga dukkanin ‘yan jiha daga kauyuka da birane don su amfana.
“Wannan yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Dauda Lawal na tabbatar da yi wa sashen kiwon lafiya garanbawul. Kuma wannan gangami na bayar da tallafin ana bada shi ne ga dukkanin jama’ar da ke ƙananan hukumomi 14.
“Ana yin wannan gangami ne a babban asibitin Gusau, babban asibitin Sarki Fahad, da kuma Asibitin Kwararru na Yariman Bakura.” In ji shi.