Sojoji sun halaka ‘yan bindiga a Zamfara

0
122

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kashe ‘yan bindiga 10 a kauyen Gadazaima na Jihar Zamfara.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce baya ga kashe ‘yan bindigar, an ceto mutum tara wadanda aka yi garkuwa da su.

Lamarin ya faru ne da safiyar Talata bayan da sojojin suka ce sun samu bayanan sirri kan shawagin da ‘yan bindigan suke yi daga Jihar Sokoto ta garin Gadazaima na Jihar Zamfara.

“Nan take sojoji suka hadu domin yi musu kwanton-bauna a cikin kauyen inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigan tsawon awa daya.

“Karfin barin wutar sojojin sun tilasta wa barayin gudawa inda suka bar wadanda suka yi garkuwa da su,” in ji sanarwar da sojojin suka fitar.

“A lokacin musayar wutan, an halaka ‘yan bindiga 10 inda wani adadi wanda ba a tabbatar na ‘yan bindigar suka tsere da raunuka.”

Sojojin kuma sun bayyana cewa akwai wasu barayin guda biyu da suka mutu a kogi a yayin da suke guduwa daga barin wutar da sojojin suke yi, inda kuma aka kama guda biyu daga cikinsu.

Akwai mutum tara da sojojin suka ce sun ceto duk da cewa ‘yan bindigar sun kashe daya yayin da ake musayar wuta da sojojin.

Bayan musayar wutan, sojojin sun kwato bindiga kirar AK 47 guda shida da bindiga mai sarrafa kanta guda daya da jigida biyar.

Sauran abubuwan sun hada da harsasai 20 nau’in 7.62MM da wayoyin salula uku da Allon sola biyu da keken dinki daya.

Haka kuma an samu miliyan biyu da dubu dari hudu da goma daga wurin ‘yan bindigan.

Ana yawan samun hare-hare na ‘yan bindiga masu satar mutane don karbar kudin fansa da kuma na ‘yan kungiyar Boko Haram a Nijeriya.

Ko a karshen watan da ya gabata sai da ‘yan bindigar suka kashe akalla mutum shida sannan suka yi garkuwa da mutum 40 a harin da suka kai a Karamar Hukumar Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna.

Sa’annan kuma a makon da ya gabata ‘yan ta’adda na kungiyar Boko Haram sun yanka manoma akalla 10 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya bayan sun kai musu hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here