Gabatar da Bazoum gaban kotu karin takalar fada ne – ECOWAS

0
174
Bazoum

Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta ce ta kaɗu da jin yunƙurin sojoji masu juyin mulki a Nijar na tuhumar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bazoum Mohamed da zargin babbar cin amanar ƙasa.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar sa’o’i bayan kalaman sojojin na yi wa Bazoum shari’a, ECOWASta ce matakin wani takalar faɗa ne daga shugabannin sojin.

Ta kuma ce hakan ya ci karo da rahotannin da ake yaɗawa cewa sabbin masu mulkin Nijar ɗin sun nuna sha’awar bin hanyar masalaha don kawo ƙarshen dambarwar da ake ciki.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara isasshiyar shaidar za a iya gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar ƙasa.
Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen ƙasar, zagon ƙasa.

Kakakin sojin Kanal Amadou Abdramane ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ta tashar talbijin ta ƙasar.

Ana sa rai, ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS za ta gudanar da wani taro ranar Litinin ɗin nan don ci gaba da matsa lamba ga sojojin juyin mulki su hau teburin tattaunawa, haka ita ma Majalisar Tsaro da Tabbatar da Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka za ta yi taron don tattaunawa a kan rikicin.


Sojojin na tsare da Bazoum da iyalansa a wani ɗaki na ƙarƙashin ƙasa a fadar gwamnati da ke birnin Yamai, tun bayan hamɓarar da shi a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin bana.

Baya ga shugaban sojojin sun kuma kama wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatinsa da ma na jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya.

Mai magana da yawun gwamnatin sojin ya ce tuni sun riga ma sun tattara duk wasu bayanai da shaidun da suke buƙata domin gurfanar da Bazoum a gaban shari’a.

A sanarwar, kakakin ya ce, za su gurfanar da Bazoum tare da waɗanda ya kira masu haɗa baki da shi a cikin ƙasar da ma ƙetare a kan laifukan da suka zayyana, saboda musayar bayanan da ya yi tsakaninsa da wasu ‘yan ƙasashen waje da shugabannin ƙasashe da kuma shugabannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya.

Bayan karɓe mulki tare da rushe zaɓaɓɓiyar gwamnatin tuni suka naɗa majalisar ministoci, tare da yin biris da duk wani kira na neman sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya, daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO da sauran ƙasashe da hukumomi masu rajin kare dimokraɗiyya na duniya.

Wannan ya janyo suka daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya.

Biris da halin ko-in-kula tare da ƙara kankane iko da kuma riƙe hamɓararren shugaban da sojin ke yi, ya sa ECOWAS ɗaukar matakai daban-daban a kan lamarin ciki har da sanya rundunar sojojinta ta ko-ta-kwana cikin shiri domin ɗaukar matakin soji a yunƙurin mayar da gwamnatin dimokraɗiyyar.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here