Ganduje ba zai hana Kwankwaso shiga APC ba – Uche Nwosu

0
146

Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon dan takarar gwamna, Uche Nwosu, ya ce shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba zai hana kowa shiga jam’iyyar ba, ciki har da shugaban jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso.

Nwosu ya ce, babu wani mutum daya da ke da jam’iyyar, inda ya kara da cewa Ganduje ba zai hana kowa shiga jam’iyyarsu ba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya kai ziyarar nuna goyon baya ga Ganduje a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, Nwosu ya ce, Ganduje zai yi alfahari da adadin mutanen da suka shiga cikin jam’iyyar a karkashin jagorancinsa.

Da aka tambaye shi, ko Ganduje zai yi amsar Kwankwaso a matsayin dan jam’iyya ganin takun sakar da ke tsakaninsu, sai ya ce “Eh. Suna da sabani a tsakaninsu amma babu wani mutum daya da zai iya hana wani shiga jam’iyyar. Hasali ma, zuwan Kwankwaso zai taimaka masa a Kano,” inda ya kara da cewa babu wanda zai yi mamakin ganin Ganduje da Kwankwaso sun warware sabanin siyasar da ke tsakaninsu.

“Za su iya warware matsalolinsu a APC,” in ji Nwosu, inda ya kara da cewa, tsarin dimokuradiyya a Afirka na bukatar karfafawa.

“Dole ne a karfafa tsarin dimokuradiyya a Afirka sabida mafi munin mulkin farar hula ya fi kyakkyawan mulkin soja.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here