Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta ce shugabannin sojin ƙasashen za su haɗu a Ghana a ranakun Alhamis da Juma’a.
Za su tattauna kan yiwuwar ɗaukar matakin soji a Nijar don mayar da ƙasar turbar dimukraɗiyya byana juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
Makwanni uku kenan da tsare Shugaba Mohamed Bazoum bayan da shugaban masu ba shi kariya, Janar Abdourahmane Tchiani, ya sanar da kansa a matsayin sabon shugaban Nijar.
Ƙasashe da dama sun yi Allah-wadai da juyin mulkin sai dai zuwa yanzu matakai ƙalilan ne na zahiri aka iya ɗauka kan sojojin da suka kifar da gwamnatin ta Bazoum.
A gefe guda kuma, Najeriya na ci gaba da jagorantar yunƙurin amfani da ƙarfin soja don tilasta wa Janar Tchiani sauka daga mulki.