Borno: Zulum ya raba tallafin buhun shinkafa da wake 4,000 a unguwar Feezan

0
227

Babagana Umara Zulum, ya gabatar da rabon kayan abinci da sauran kayan agaji ga talakawan jiharsa 2,000 dake zaune a unguwar Feezan da ke birnin Maiduguri.

Rabon tallafin da aka gudanar a ranar Laraba a kwalejin koyon shari’a da addinin musulunci ta Mohammed Goni na daga cikin kokarin da ake na rage wahalhalun da tsadar rayuwa da ake fuskanta sakamakon janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

A watan Yuli da ya gabata ne Zulum ya gabatar da rabon kaya wa gidaje sama da 300,000 tare da mutane kusan shida a kowane gida don kai wa mabukata miliyan 1.8.

A karkashin tsarin, ya dace duk wani mazaunin Feezan ya karbi kayan abinci domin rage wahalhalu sakamakon tashin farashin kayayyaki da ake fama da shi.

A sabon rabon da gwamnan ya gabatar a Feezan ga gidaje 2,000 da suka kunshi magidanta maza 1,000 da kuma mata 1,000 kowannensu ya samu buhun shinkafa da buhun wake guda guda.

Domin a samu tsarin tabbatuwar gaskiya da rikon amana a tsarin, gwamnatin jihar Borno ta saka wasu amintattu matsayin kungiyoyin farar hula da za su kasance cikin kwamitin raba kayan na agaji.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Zulum wanda kwamishinan kula da kananan hukumomi da masarautu, Hon. Sugun Mai Mele, ya ce unguwanni 15 a cikin birnin Maiduguri za su ci gajiyar inda kowace shiyya za ta karbi buhun shinkafa 2,000 da buhun wake 2,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here