Wani magidanci ya gama alkali da Allah kan ya raba shi da matarsa

0
125

A babban birnin tarayya Abuja ne wani magijanci ya garzaya kotu ya samu alkali ya gama shi da girman Allah kan ya raba aure tsakaninsa da matarsa.

Wannan magidanci ya bukaci haka ne domin baya da wani zabi sama da hakan domin ita dai wannan mata bata da aiki daya wuce da zarar ya aikata wani abu dan kadan ta dinga falla masa mari.

Magidancin mai suna Rafeal Ciyama  ya maka matar tasa kotun dake babban birnin tarayya Abuja idna ya ce matar tasa bata ganin girmansa balle na iyayensa a matsayinsa na mijinta.
 
Ya kara da cewa ga kotu ko da yaran da suka haifa bata kula da su ga ta da saurin hannu dazar ya dan yi wani abu sai ta falla masa mari idan kuma ya kuskura ya tanka sai ta zage damtse ta masa duka domin ta fi karfinsa wanna shine dalilin da ya sa ya zo kutu yake rokon a raba wannan auren kawai kowa ya huta.

Sai dai ita a nata bangaren ta musanta zarge-zargen da mijin nata yake mata inda tace ita har yanzu tana kaunar mijin nata, anan alkalin kotun Justice Dada Oluwa ya shawarce su da su koma gida su samar wa junansu daidai to, idan kuma hakan ya gagara samuwa sai su dawo gabansa ya yi musu hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here