Makasudin cin bashin gaggawa na Dala biliyan 3 da NNPC yayi

0
169

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited ya sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar ciyo bashin gaggawa daga bankin raya kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki na Afirka, wato AFREXIM Bank.

Bashin wanda ya kai dala biliyan uku, za a yi amfani da shi wajen biyan kudin danyen mai da ake bin kamfanin na NNPC bashi.

Abin da kuke bukatar sani game da wannan lamuni na gaggawa da NNPC ya samu.

Shin wannan rancen zai shafi farashin man fetur?

Wannan rancen zai karfafa Naira, a sakamakon wannan shiri za’a samu raguwar farashin mai. Hakan na nufin idan darajar Naira ta kara daraja, farashin man fetur zai ragu kuma farashin zai daina karuwa.

Shin wannan rancen zai dawo da tallafin mai da aka cire ?

A’a. Zai kara karfin Naira, zai haifar da raguwar farashin man fetur daga matakin da ake akai yanzu, wanda zai sa dawo da tallafin mai ba dole ba ne.

Ta yaya za a biya bashin?

Za a biya lamunin bashin ne bisa wani kaso na kudaden da za’a samu daga hako danyen mai a nan gaba. Hanya ce mai muhimmaci wacce ke tabbatar da daidaito tsakanin bukatun tattalin arzikinmu na yanzu da kuma damar samar da kayayyaki a nan gaba.

Menene bambanci tsakanin wannan da yarjejeniyar musanye da ta gabata?

Wannan ba danyen mai ba ne, don yarjejeniyar samfuran da aka tace inda saboda gwamnati bazata samu wani kudi daga musayar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here