Inter Miami ta lashe gasar Leagues Cup

0
275

Kungiyar kwallon kafar Inter Miami da shahararren dan kwallon karar nan Lionel Messi ke taka leda sun lashe Kofin Leagues Cup ranar Asabar bayan sun doke Nashville da ci 10-9 a bugun fenareti.

Kungiyoyin biyu da suka kara da juna sun yi bugun fenareti ne bayan wasan ya tashi da ci 1-1.

Messi ne wanda ya zura kwallon farko a minti na 24 da fara wasa sai dai kuma daga bisani Fafa Picault ya farke wa Nashville wannan kwallo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Bayan Leonardo Campana ya kasa yin amfani da damarsu ta karshe, an tafi bugun fenareti wanda hakan ya kai ga har sai da gololi biyun kungiyoyin buga fenareti – amma golan Inter Miami Drake Callender ya kade kwallon da takwaransa na Nashville Elliot Panicco ya doka masa.

Lionel Messi ya taka rawar gani irin ta masu kwarewa sosai yayin ya ci kwallaye goma a gasar Leagues Cup da ya buga wa Inter Miami.

Tsohon dan wasan na Barcelona, wanda yai zakakurancin lashe kyautar ballon d’or har sau bakwai, ya zura kwallo cikin duk wasanni bakwai da ya buga wa kungiyar Inter Miami tun daga sanda ya soma murza leda a kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here