Shugaban kasar Gambiya ya hana jami’an gwamnati tafiye-tafiye don rage kashe kudi

0
147
Adama Barrow
Adama Barrow

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya dakatar da kansa da dukkan jami’an gwamnatinsa yin balaguro zuwa ƙasashen waje don rage kashe kudin gwamnati.

A cewar mai magana da yawunsa, Shugaba Barrow “ya saka hannu kan umarnin shugaban ƙasa na dakatar da shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa, ministoci, manyan jami’an gwamnati, da ma’aikata daga tafiye-tafiye a shekarar kasafi ta bana”.

Sai dai kamfanin labarai na AFP ya ruwaito Mista Ebrima Sankareh na cewa ganawar da ta zama dole a ƙasashen waje kuma wadda ba gwamnati ce za ta ɗauki nauyinta ba, babu laifi.

Gambiya da ke da mutum ƙasa da miliyan biyu, ita ce ta 174 cikin ƙasashe 191 da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bayyana a matsayin masu arziki.

Sakamakon kuɗin shiga da ke raguwa a ƙasar da kuma maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a kan tallafin man fetur, da kuma na takin zamani da hatsi, kasafin kuɗin ƙasar ya samu giɓi a shekarar da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here