Ba mu lamince sojojin Nijar su ci gaba da mulki har shekara uku ba – ECOWAS

0
132
ECOWAS-chairman-Bola-Tinubu

Kungiyar ECOWAS ta ce ba za ta amince da maganar da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi ba, cewa zai mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyayya cikin shekara uku masu zuwa.

Cikin wata sanarwa da shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahmane Tchiani ya fitar da maraicen ranar Asabar ya ce zai miƙa mulki hannun farar hula cikin shekara uku.

A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan harkokin siyasa da tsaro da tabbatar zaman lafiya na ECOWAS, Abdel-Fatau Musa, ya ce yana ganin sanarwar da Janar Tchiani ya fitar dabara ce ta buƙatar tattaunawa.

Ya ƙara da cewa ya kamata a ce jagororin sojin Nijar sun mayar da hankali wajen yaƙar ‘yan ta’adda, maimakon harkokin mulkin ƙasar.

Ƙungiyar dai na buƙatar sojojin su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba.

ECOWAS ta kuma yi barazanar amfani da ƙarfin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

To sai dai cikin sanarwar da ya fitar, ranar Asabar, Janar Tchiani ya yi gargaɗin cewar amfani da ƙarfin soji ka iya wargaza zaman lafiyar ilahirin yankin yammacin Afirka.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here