Gwamnatin tarayya ta ce babu wani shirin sake maido da tallafin man da ta cire jim kadan bayan karbar ragamar mulki, duk kuwa da yadda al’ummar kasar ke korafe korafe a game da irin halin kuncin da matakin ya jefa su.
Babban mai taimaka wa shugaba Bola Tinubu a fannin yada labarai, Tope Ajayi ne ya bayyana haka, a lokacin da yake mayar da martani ga rade-radin da ake yi cewa gwamnatin kasar za ta lashe aman da ta yi a game da wannan mataki nata.
Tun da farko sai da shugaba Tinubu, ta bakin kakakinsa, Ajuri Ngalale ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa ba za a kara farashin man fetur ba.
“Shugaba Tinubu ya gamsu bisa ga bayanin da ke gabansa cewa za mu iya kula da farashin a yanzu ba tare da musanya tsarin da aka bullo da shi na yanzu ba ta hanyar hanzarta tsaftace rashin aiki bangaren man fetur,” in ji Ajayi.
Tun a ranar 29 ga watan Mayu da aka rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa a lokacin ya bayyana cire tallafin man fetur, farashin da ya ninka sau uku: daga kimanin N200 zuwa kusan N600.
Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tabarbarewar tattalin arzikin miliyoyin ‘yan Najeriya.