Abdulsalami ya mika wa Tinubu rahoton ziyarar da suka kai Nijar

0
160
ECOWAS
ECOWAS

Shugaban tawagar da kungiyar ECOWAS ta tura zuwa Nijar domin tattaunawa da shugabannin sojin kasar Abdulsalami Abubakar, ya ce yana ganin za a samu mafita daga wannan takaddarmar ba tare da amfanin da karfin soja ba.

Janar Abdulsalami mai ritaya ya faɗi haka ne bayan da ya miƙa wa Shugaban kungiyar Bola Tinubu rahoton ziyarar da suka kai Nijar a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Ya ce ziyarar da suka kai Nijar ta yi alfanu sosai kuma hakan ya buɗe kofar tattaunawa da za ta sanya a warware rikicin.

A yayin ziyarar dai tawagar ta gana da shugaban gwamnatin sojin Abdurrahman Tchiani da kuma hamrarren shugaban kasar Mohammed Bazoum:

“Mun fara tattaunawa da sojojin, sun kuma faɗi maganganu da dama. Rahoton abin da ya wakana ne na kawowa shugaban ƙasa,” in ji Abdussalam.

Ya ce za su yi duk abin da ya kamata don ganin an bi hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin ba tare amfani da karfi ba.

“Ba bu wanda yake son shiga yaƙi, saboda ba shi da alfanu. Amma, shugabanninmu sun faɗa cewa muddin hanyar diflomasiyya ta ki aiki, to fa akwai alamar amfani da karfi”.

Cikin waɗanda suka halarci ziyarar miƙa wa shugaba Tinubu rahoton, akwai shugaban hukumar Ecowas, Dakta Omar Touray, da shi shugaban tawagar da ECOWAS ta tura Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar da kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here