An dawo da ‘yan Najeriya 161 daga Libya

0
89
Yan Najeriya
Yan Najeriya

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, an mayar da wasu ‘yan Najeriya 161 daga kasar Libya zuwa gida, a wani shirin sa-kai da Majalisar Dinkin Duniya ke tallafawa.

Sun isa ne a wani jirgi daga Tripoli zuwa babban filin jirgin saman Legas ranar Litinin.

Daga cikin wadanda aka mayar da su ɗin akwai mata 75 da ƙananan yara shida wadanda aka tsare a wuraren tsare mutane a ƙasar Libya.

Ministan cikin gidan ƙasar ya bayyana cewa, an dakatar da mutum 102 daga cikin waɗanda aka mayar da su gida a kan iyakar Libya da Tunisia.

Libya dai ta kasance wata babbar hanya da bakin haure ‘yan Afirka ke bi a Æ™oÆ™arinsu na tsallakawa Turai ta tekun Bahar Aswad ba bisa Æ™a’ida ba.

Wani jami’i a ofishin jakadancin Najeriya a Libya, ya tabbatar wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa baÆ™in hauren sun zaÉ“i koma wa gida ne da son ransu, ba tare da an tilasta musu ba.

Ya kuma bayyana cewa waɗanda suka koma ɗin sun gamsu su koma Najeriya, domin “babu wani wurin zama kamar gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here