Muna da shawarwarin magance matsalar tsaro a Najeriya – Kungiyar Fulani

0
125
Fulani Makiyaya
Fulani Makiyaya

Kungiyar makiyaya ta Kullen-Allah ta kasar ta yi kira ga illahirin makiyayan kasar da su guji duk wani abu da zai kai ga tayar da zaune tsaye.

Kungiyar ta bayar da tabbacin tana da shawarwarin da za ta bayar, wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin Najeriyar.

Kungiyar dai ta bayyana hakan ne a karshen wani babban taro da ta yi a birnin Maiduguri na jihar Barno, kuma shugaban kungiyar Honarabul Khalil Muhammad Bello ya shaida wa BBC cewa sun kira taron ne domin lalubo hanyoyin zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma da ƙasa baki ɗaya.

Honarabul Khali ya ce sun kuma tattauna kan yadda za a guje wa yin duk wata zanga-zanga a Æ™asar, saboda sun yi la’akari da abin da zanga-zanagar kwanakin baya ta haifar na rashin zaman lafiya, ” mun fahimci hakan babu abin da zai yi illa Æ™ara jawo matsala a Æ™asar”.

Taron ya kuma duba batun tsaro da ke addabar Najeriya musamman yankin Arewa, inda ƙungiyar ta ce tana da shawarwarin da za ta ba gwamnatin Najeriya da za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.

“Idan har gwamnatin tarayya a shirye take to wallahi a shirye muke mu ba ta shawarar ta hanyar salama ba tare da ta kashe kudade ba ta hanyar Fulako,” cewar Honarabul Khalil.

Ƙungiyar ta ce cikin wata biyu idan har gwamnati ta bi shawararta za a samu zaman lafiya tsakanin al’ummomin da ba sa ga maciji da juna, ” Mu muna da ruwan zaman lafiya da za mu yayyafa wa Najeriya ta dinke ta sake zama abu guda.”

Fulani dai wata ƙabila ce da ake zargi da tada zaune tsaye a Najeriya musamman yankin arewacin ƙasar, wajen satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma hana manoma a karkara noma da kiwo da ma zama a yankunan.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here