Rundunar sojin Najeriya ta bukaci EFCC ta zakulo masu daukar nauyin ta’addanci a kasar

0
180

Rundunar sojin Najeriya ta bukaci Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa ta Kasar EFCC, ta rika bubiyar mutanen da ta kira makiya ƙasar da ke ɗaukar nauyin ta’adanci a ƙasar.

Babban hafsan sojin ƙasar, Janar Christopher Musa, ne ya yi kiran a shalkwatar tsaro ƙasar da ke Abuja a lokacin da ya karbi baƙuncin shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede.

Janar Christopher Musa ya ce bibiyar waɗanda ke ɗaukar nauyin ta’addanci don gano su, hanya ce ƙwaƙƙwara ta yaƙi da ta’addanci a faɗin duniya, wadda sojoji ne suka gano ta.

Babban hafsan sojin ya buƙaci EFCC ta ƙarfafa wa masu riƙe da mukamai gwiwa wajen gudanar da ingantaccen shugabanci don inganta harkokin tatalin arziki da tsaron ƙasar.

Ya ƙara da cewa rundunar sojin ƙasar na aiki tare da baban kamfani mai na ƙasar NNPCL da sauran masu ruwa da tsaki a kowace rana don yaƙi da masu satar mai a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here