‘Yan bindiga sun sake sace mutane a Kaduna

0
145
Kaduna

Rahotanni na daga jihar Kaduna na cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum fiye da 80 a garin Kajuru a wani sabon hari da suka kai garin ranar Lahadi.

Harwayau, ‘yan bindigar sun fasa shaguna inda suka saci kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki kamar yadda wani shaida ya fada wa BBC.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansur Hassan ya tabbatar da sace mutanen ga BBC sai dai bai fadi yawan adadin da kafafen watsa labarai ke ambatawa ba.

Hassan ya ce nan ba da jimawa ba za su sanarwa da manema labarai da jama’a iya adadin mutanen da aka sace kasancewar har yanzu ana tantancewa.

“Eh, gaskiya mun samu wannan labari na masu garkuwa da mutane sun sake sace mutane da dama, amma har yanzu ba a san iya adadin mutanen da aka sace ba saboda daji ne gurin.” in ji Hassan

“Shiyasa kullum muke kira ga jama’a da cewa duk lokacin da suka ga gittawar waÉ—annan mutanen, ba sai laile sun kai hari ba, a yi Æ™oÆ™ari a sanar da mu saboda irin waÉ—annen wurare daji ne sosai”

“Saboda kusan yaÆ™in da ake yi da waÉ—annan Æ´an ta’adda da kusan jama’an gari ake yi.

Hassan ya ce rundunar jihar ta tura Æ™arin jami’an tsaro don bin sawun mutanen da aka Æ™ara sacewa.

Harin dai na zuwa ne ƙasa da kwana biyu bayan an sace wasu mata fiya mata 15 tare da wani namiji ɗaya a ƙauyen Dogon Nama duk dai a ƙaramar hukumar ta Kajuru.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here