‘Bana tsammanin yan Delta ne suka hallaka sojojin Najeriya’ – Akpabio

0
157

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa mutanen da suka yi wa sojojin ƙasar 17 kisan gilla a jihar Delta na iya zama sojojin haya ba wai mutanen yankin Neja Delta ba.

Ya bayyana haka ne a zaman majalisar na ranar Talata, kwana biyar kenan bayan faruwar mummunan harin.

Akpabio ya yi tsokacin ne lokacin da majalisar ta yanke shawarar kafa kwamiti domin gano abin ya janyo kashe sojojin.

Ya ce “Ba na son na yanke hukunci cewa waɗan nan mutanen daga yankin Neja Delta suka fito saboda muna mutunta mata da zama masu kayan sarki. Shi ya sa nake cewa abin da za ku nema shi ne a gudanar da cikakken bincike domin gano ko sojojin haya ne daga wasu ƙasashen da suka zo Najeriya su aikata ta’annatin saboda bana tunanin mutane ne ƴan Neja Delta.

“Ba ma cikin yaƙi. Ko a lokacin yaƙi, ba zai yiwu a rasa irin wannan adadi na sojoji ba. Babu wani yanki da zai aikata irin wannan, ba na tunanin ƴan Neja Delta ne. Don haka, abu na farko shi ne mu lalubo mutanen da suka aikata taɓargazar.” in ji Akpabio.

Ya ce kwamitin zai ɗauki nauyin tabbatar da cewa an hukunta mutanen da ke da hannu a kisan jami’an.

Tuni dai kalaman na shugaban majalisar suka soma yamutsa hazo a Najeriya inda ƙungiyoyin farar hula da masu amfani da shafukan sada zumunta suke ta bayyana rashin jin daɗinsu ga kalaman na Akpabio.

An kashe sojojin ne a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a yankunan Okuoma da Okoloba da ba sa ga maciji da juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here