Najeriya na fuskantar koma baya a yaki da cutar tarin TB – WHO

0
278
Tarin TB

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta koka da samun koma baya a yaki da tarin fuka a Najeriya sakamakon karancin kudaden tafiyar da gangamin yaki da cutar wanda ya kunshi samar da magunguna rigakafin da na rage kaifin cutar mai saurin yaduwa.

Dai dai lokacin da Duniya ke shirin bikin ranar yaki da cutar ta tarin fuka ko kuma Tuberculosis a ranar 24 ga watan nan, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce Najeriya na ganin koma baya a yaki da cutar wanda ke diga ayar tambaya kan kudirin kasar na fatan kawo karshen cutar nan da shekarar 2030.

Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin WHO da KNCV da kuma kungiyoyin da ke taimakawa wajen fafutukar yaki da cutar da ya gudana a Abuja, dukkaninsu sun bukaci mahukuntan kasar da masu ruwa da tsaki sum ara baya wajen ganin bayan cutar ta tarin fuka.

A cewar WHO rashin wayar da kai musamman a yankunan karkara na ta’azzara yaduwar cutar wadda wani kan gogawa wani ta hanyar cudanyar lumfashi, cutar da kuma ke matsayin ta 10 a jerin cutuka mafiya kisa a Duniya.

Yanzu haka dai Najeriya na matsayin ta 6 cikin kasashe 30 da ke fama da yawaitar masu dauke da cutar ta tarin fuka, yayinda kasar mafi yawan jama’a a Afrika ke matsayin lamba daya wajen yawan masu fama da cutar a nahiyar.08 / 1:01

Nahiyar Afrika na ganin sabbin kamuwa da tarin tb miliyan 2 da dubu 400 kowacce shekara da fiye da dubu 479 daga Najeriya kasar da ke ganin mutuwar akalla mutum dubu 97 da 900 duk shekara sanadiyyar Cutar.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here