Yan bindiga sun aikata kazamin hari kan masu shirin buda baki a Zamfara

0
172

Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari garin Ɓaure da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afkawa garin da yammacin ranar Talata, lokacin da mutane ke hada-hadar yin buda baki, tare da buɗe wutar harbin kan mai tsautsayi.

Wani mazaunin garin da BBC ta zanta da shi da muka sakaya sunan shi, ya ce su na zaune da yammacin Talata sai aka fara cewa ga ɓarayi nan sun shigo, nan take kuma suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

”Da suka fara harbe-harben mun rasa mafita, sai makwaftanmu suka kawo mana dauki, anan dai suka kashe mutum biyu da jikkata wasu biyar.

Cikin wadanda suka kashe akwai Aliyu Abubakar daga gidan Zuma, sai kuma Barkono Musa daga Suto ta kasar Kwatarkwashi, sauran biyar kuma su na kwance a asibiti,” in ji mutumin.

Ya kara da cewa ɓarayin dajin sun zo akan babura talatin, dauke da muggan makamai, haka sukayi ta ɓarin wuta a ciki da wajen gidaje.

Wani shi ma da ya shaida abin da ya faru, ya ce da fari akan babura biyu suka shiga garin na Ruwan Ɓaure, suka tambayi wadanda suka samu zaune ina nasu kason na tallafin da aka bai wa mutanen garin.

”Mun dauka su biyu ne kaɗai sai muka bi su da gudu, ashe sun yi mana kwantan ɓauna, sai ganinsu muka yi babura talatin su ka fara harbin kan mai tsausayi, suka kewaye garin, haka suka kashe mutum biyu da azumi a bakinsu, bayan wadanda suka raunata da ke samun kulawa a asibiti.

Iyalan wadanda suka kashe na cikin mawuyacin hali, saboda hatta abin da za su ci dakyar ake samunsa.

“Mutane sun rinka yanke jiki suna suma saboda gigicewa da dimauta kan halin da suka samu kan su a ciki.”

BBC ta tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar, da mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris, sai dai sun bukaci a ba su lokaci domin su yi bincike.

Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.

Sai dai gwamnatin jihar da ta tarayya da jami’an tsaro na cewa su na bakin kokari domin magance matsalar, a wasu lokutan ma jami’an tsaro kan sanar da nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar.

A baya-bayan nan gwamnatin Gwamna Dauda Lawan Dare ta kaddamar da rundunar ‘yan sa kai da ta yi wa lakabi da Askawarawan Zamfara domin taimakawa jami’an tsaro magance matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here