Tinubu ya nemi yan majalisa su daina yawan gayyatar ministoci

0
106

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ƴan majalisar wakilan ƙasar su daina yawan kiran ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya don titsiye su a gaban kwamitocin majalisar. 

A yayin da yake buɗe-baki da ƴan majalisar a ranar Laraba da maraice a fadar gwamnatin ƙasar, Shugaba Tinubu ya ce duk da cewa sa ido yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin harkokin mulki, yawan kiran jami’ai na iya kawo cikas ga ayyuka da kuma yi wa ƴan ƙasa hidima.

“Na daɗe ina kallon yadda kwamitoci daban-daban suke kiran ministoci da shugabannin hukumomi. Na yi wa Shugaban Majalisa ƙorafin cewa su bar su su sha iska. Su bar mutanen nan su yi aikinsu. Ba muna cewa ba ku da tasiri ba ne. Ba muna cewa ba za ku iya sa ido ba. 

“Amma ku yi la’akari da aikin farko na kowace hukuma da ma’aikatanta, ko irin nauyin da ke kan Gwamnan Babban Banki ko Babban Ministan Tattalin Arziki da Ma’aikatar Kuɗi a gare ku da sauran al’umma baki ɗaya,” kamar yadda sanarwar da mai taimaka masa kan harkon watsa labarai ta ambato shi yana cewa. 

Shugaban ƙasar ya buƙaci ƴan majalisar da su nuna hazaƙa wajen gudanar da ayyukansu na sa ido. 

“Idan ana raba musu hankali ko damun su, wataƙila za mu sauya salon zaman majalisa zuwa cikin tsawon dare. Dole ne mu nemo hanyar da za mu yi mu’amala mai kyau da juna. Wannan roƙo ne gare ku.

“Ku duba ku ga ko za ku iya yarda su aika wakilai a wasu lokutan ko kuma su aike muku takardu,” in ji Shugaban ƙasar, yana mai roƙon majalisar wakilan a kan batun. 

Yayin da yake bayyana ƙwarin giwar da yake da ita a kan Majalisar Dokoki ta ƙasa wajen tabbatar da shugabanci na gari, Shugaba Tinubu ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa. 

Ya ce haɗin gwiwar aiki da aka samu ya haifar da gaggauta amincewa da wasu ƙudurori don inganta jin daɗin ƴan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here