Yan sanda sun gurfanar da jaruma Amal Umar a gaban kotu bisa yunkurin bada cin hanci 

0
311

Rundunar Yan sandan Najeriya, shiya ta daya dake kula Kano da Jigawa, wato Zone 1 Kano, ta gurfanar da jarumar fina-finan Hausar Kanywood , mai suna Amal Umar, a gaban kotun majistiri mai Lamba 24, bisa zargin ta da yunkurin bayar da cin hanci na naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) ga wani jami’an dan sanda mai suna ASP Salisu Bujama, don ya rufe binciken wasu kudaden kasuwanci da ake zargin saurayin ta da karkatarwa.

Wani mai suna Alhaji Yusuf Adamu, ne, ta hannunsa lauyan H.I. Dederi, ya shigar da korafi ,ga mataimakakin sufeton Yan sandan Najeriya dake kula da shiya ta daya, AIG Umar Mohd Sanda, a ranar 18 ga watan Ogustan 2022, da cewar, wani Ramadan Inuwa, ya karbi kudin kasuwancin wayoyin salula har Naira miliyan arba’in, amma tunda ya Karba bai sake ganinsa ba.

A tattaunawar da Jaridar Idongari.ng, ta yi da mai magana da yawun rundunar Yan sandan Najeriya shiya ta daya (Zone 1 Kano ) CSP Bashir Muhammed, ya shaida cewa , binciken Yan sandan, ya gano an tura wa Amal Umar naira miliyan 13 cikin asusun bankin ta.

CSP Bashir, ya ce sun gaiyaci Amal Umar, domin ta amsa wasu tambayoyi, kuma bayan haka sun bayar da belin ta, sai dai ba su barta ta tafi da Wata mota, mai namba NSR 858JH, da ake zargin saurayin ya siya mata.

” Kudin da suke cikin Asusun banki na, na saurayi na ne”cewar Amal Umar amma naira miliyan takwas ne “.

Tun daga lokacin da aka bayar da belin Amal Umar, ne ta garzaya gaban Wata babbar kotun jahar Kano, don Hana Yan sanda ci gaba da gudanar da bincike akanta.

Inda kotun ta dakatar da jami’an Yan sandan kan Ci gaba da gudanar da bincike kan Amal Umar mazauniyar Tishama Hotoro Kano.

Wannan damar ce ta ba wa, yar wasan Hausar zuwa rundunar shiya ta dayan, don ta karbi motarta , har ta yi yunkurin bayar da cin hanci Naira dubu dari biyar (N500,000:00) ga jami’in dan sandan da yake bincike wato ASP Salisu Bujama.

Amal , ta bayar da Kafin alkalamin naira dubu dari biyu 250,000 da nufin za ta ciko ragowar , inda dan sandan ya Kama ta da hujjar da za ta sanya a gurfanar da ita a gaban kotu.

Kakakin rundunar Yan sandan shiya ta daya CSP Bashir Muhammed, ya ce wannan dalilin ne , ya sanya suka gurfanar da jarumar fina-finan Hausar , a gaban kotun majistiri dake unguwar gyadi-gyadi Kano , bisa zargin ta da yunkurin bayar da cin hanci ga jami’in dan Sanda Wanda yin hakan ya Saba da sashi na 118 na kudin Penel Code.

CSP Bashir Muhammed, ya ce , mataimakin sufeton Yan sandan Najeriya AIG Umar Mohd Sanda, ya gargadi Yan sandan shiyar su ci gaba da yakar cin hanci da rashawa, wanda shi ne zai sanya a yi wa, Wanda aka zalinta adalci , kamar yadda Babban sufeton Yan sandan Najeriya IGP Kayode Adeolu Abegketun, ya bayar da umarni.

A karshe ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike kan kudin da ake zargin sun yi batan dabo tsaninta da saurayin ta, don ba wa Kowa hakkinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here