Dole ne a hukunta wadanda suka kashe mana sojiji 17 – Tinubu

0
156
Tinubu
Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce waɗanda suka kashe sojoji a jihar Delta za su fuskanci hukunci, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kai hare-hare kan sojoji da ababen more rayuwa ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar dattawan kasar a yayin wani zaman cin abincin buɗe baki a fadar gwamnati a ranar Alhamis.

Tinubu ya ce sojoji za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatinsa wajen kawar da barazanar tsaro a faɗin kasar.

“Rundunar sojojinmu na aiki tukuru, kuma ba za mu bar maharan su lalata mutunci da ƙimar sojojinmu da kuma shugabancinta ba.”

“Za mu ci gaba da karfafawa da gwagwarmayar neman ƴancinmu da haƙƙinmu na zama daya, kuma za mu yi nasarar kawar da talauci daga kasarmu,’’ in ji Tinubu. Shugaba.

Tinubu ya shaida wa shugabannin Majalisar Dattawan cewa, mutuncin Majalisar Dokoki dole ne ya ci gaba da wanzuwa, kuma a ko da yaushe gwamnatinsa za ta ƙarfafa hadin gwiwa don ci gaban kasa.

“A kan matsalar tattalin arziki da muke fuska ya yanzu, muna ƙoƙarin gaske don ganin mun magance wannan matsalar, kudaden shigarmu sun inganta.”

“Abin da ya kamata mu yi shi ne mu kula da yadda muke kashe kuɗaɗe da kuma yadda za mu sarrafa kanmu da kyau.”

“Nan ba da jimawa ba za ku ga sauyi, murmushin ‘yan Najeriya ya kusan dawowa,” in ji shugaban.

A nasa jawabin, shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya godewa shugaba Tinubu bisa karbar bakuncin ‘yan majalisar, inda ya bayyana cewa yin mu’amala akai-akai zai ƙara fahimtar juna da gudanar da shugabanci mai inganci.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here