Hukumomin Nijar ba su gaya wa dakarunmu su fita daga kasar ba – Amurka

0
133

Wata babban jami’a a Hedkwatar Tsaron Amurka ta shaida wa ƴan majalisar dokokin ƙasar ranar Alhamis cewa a hukumance sojojin Nijar ba su bai wa dakarun Amurka umarnin barin ƙasar ba, tana mai cewa ta samu bayanai masu harshen-damo kan matakin korar dakarun nasu daga Nijar.

Celeste Wallan der, mataimakiyar sakataren tsaron Amurka kan ƙasashen duniya, ta shaida wa Kwamitin Harkokin Sojoji na Majalisar Wakilan ƙasar cewa a hukumance kawo yanzu gwamnatin sojojin Nijar, wadda aka fi sani da CNSP, ba ta umarci sojojin Amurka su fita daga ƙasar ba.

Wallander ta ce gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar da ta bai wa dakarun Amurka damar zama a  ƙasar. Amma ta ce sojojin sun “tabbatar mana cewa za a kare lafiyar dakarun Amurka  kuma ba za su ɗauki wani mataki da zai cutar da su ba.”

Amurka tana da dakaru kusan 650 tare da ɗaruruwan masu taimaka musu a Nijar, inda suke yaƙi da ta’addanci. Sai dai a watan Yulin da ya gabata sojoji sun kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya sannan daga bisani suka kori dakarun Faransa daga ƙasar.

Wallander ta ce Amurka tana yin nazari kan wasu hanyoyi na ci gaba da yaƙi da ta’addanci a yankin.

Yawancin dakarun Amurka da ke Njar suna zaune ne a sansani guda ɗaya kuma suna ci gaba da gudanar da aiki da jirage marasa matuƙa, ko da yake suna yin hakan ne da zummar bai wa kansu kariya, a cewar mataimakiyar kakakin hedkwatar tsaron Amurka Sabrina Singh.

“Ana ci gaba da tattaunawa da gwamnatin soji ta CNSP domin samun mafita,” in ji Singh.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here