Tinubu ya bayyana hanyar da darajar Naira zai dagu

0
286
Naira
Naira

Fadar shugaban kasar ta yi imanin cewa muddin yan Nigeria suka fara sayan kayan da ake samarwa a kasar darajar Naira zata farfado cikin kankanin lokaci.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai da ya yi da manema labaran fadar shugaban kasa ranar Juma’a.

“Za mu iya dawo da darajar Naira idan har mun Amince Zamu rika sayan duk kayan da ake samarwa a Nigeria.”

Ya ce wannan na daya daga cikin shawarwarin da shugaba Tinubu ya dauka na ganin an ci gaba da farfado da darajar Naira ta Najeriya a kan sauran kudaden duniya.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai ya kuma bayyana irin ayyukan da gwamnatin take baiwa kanana da matsakaitan yan kasuwar duk da zummar farfado da tattalin arzikin kasar.

Ya ce shugaban kasar na yin duk mai yiwuwa wajen sauke nauyin da ke kan sa tare da tabbatar da cewa ya dora wa ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya suna kashe kudaden su yadda ya Kamata.

Ya bayyana hakan ne ta hanyar tabbatar da rage yawan kudaden tafiye-tafiye, tare da tabbatar da cewa da dokar hana tafiye-tafiye zuwa kasashen waje na wucin gadi da aka sanya daga ranar 1 ga Afrilu, kan duk masu rike da mukaman gwamnati wanda hakan zai taimaka wajen adana sama da Naira biliyan 5 a duk watanni uku.

Game da batun mafi karancin albashi, Ngelale ya ce shugaban kasar na son dawo da martabar kuɗin kasar kafin fara amfani da sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here