Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wata motar haya mallakar Hukumar Sufuri Ta Jihar Katsina (KTSTA) inda suka yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na daren ranar Alhamis.
Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a tsakanin ƙauyukan Burdugau da ‘Yargoje da ke kan hanyar Ƙanƙara a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara.
Wani ma’aikacin KTSTA wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, motar ta taso ne daga Funtuwa zuwa Katsina lokacin da lamarin ya faru.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar ASP Aliyu, an yi garkuwa da fasinjoji takwas a cikin motar bas ɗin amma ‘yan sanda sun samu nasarar ceto huɗu.
“Muna kan batun. Jami’anmu sun ceto mutum ɗaya da mata uku da aka kwashe, kuma har yanzu muna kan aikin kuɓutar da sauran huɗun,” in ji shi.