Dalibai sun mutu a turmutsutsun karbar tallafin abinci a jami’ar Keffi 

0
182

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana kaɗuwarsa a kan mutuwar wasu ɗailbai na Jami’ar Keffi, waɗanda suka rasa rayukansu a wajen rububin karɓar tallafin kayan abinci da gwamnati take rabawa. 

Lamarin ya faru ne a yau Juma’a da safe, inda ɗalibai biyu mata suka mutu.

A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar don nuna alhini kan batun, ta ce an samu turmutsutsun ne bayan da wasu ɓata-gari da wasu ɗalibai marasa kan-gado suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin harabar babban filin taro na makarantar don kwashe shinkafar da aka ajiye da nufin raba wa ɗalibai a matsayin tallafi. 

“Wannan mummunan abu ya faru ne awanni kaɗan kafin a fara rabon tallafin wanda aka tsara za a yi shi da safe, in ji sanarwar. 

Ta ƙara da cewa “Gwamna Sule ya ji matuƙar takaici na mutuwar ɗalibai biyu na jami’ar a wannan turmutsutsun da ya faru sakamakon aikata laifi. 

“Ina addu’ar Allah Ya ji ƙansu, Muna kuma miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalai da ƴan’uwa da abokan mamatan. Waɗannan matasa sun haɗu da ajalinsu a wani yanayi mai ciwo.” 

Tuni gwamnan ya bai wa hukumomin Jami’ar Keffin da na tsaro umarnin fara bincike ba tare da ɓata lokaci ba a kan lamarin don gano waɗanda suka jawo shi.

Duk wanda aka samu da hannu a kan lamarin za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Rabon tallafin na cikin shirin Gwamna Sule na bai wa ɗaliban makarantun gaba da sakandare na jihar shinkafa da kuma naira 5,000 ga kowannensu.

Gwamnatin jihar ta ce an samu nasara a rabon da aka yi a sauran makarantu kamar su Jam’iar Tarayya ta Lafia da Isa Mustapha Agwai Polytechnic ta Lafia, da Kwalejin Aikin Gona da Kimiyya da Fasaha ta Lafia da Makarantar Koyon Aikin Jinya da kuma Kwalejin Ilimi ta Akwanga. 

Sai kuma Federal Polytechnic, Nassarawa da Kwalejin Fasahar Lafiya ta Keffi.

TRT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here