Gwamnatin Najeriya ta jajanta wa Rasha kan harin da aka kai wani gidan rawa

0
227
Tinubu
Tinubu

Najeriya ta aika sakon ta’aziyya tare da jaje ga shugaban ƙasar Rasha Vladmir Putin, kan harin da aka kai wani gidan rawa da ke kusa da birnin Moscow.

Cikin wani sakon X da ya wallafa, Ministan harkokin Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce Najeriya da mutanenta na jajantawa Rasha kan kisan mutanen da aka yi wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da kuma gwamman da aka jikkata.

“Gwamnati da mutanen Najeriya na nuna alhini ga mutanen da wannan mummunan hari ya rutsa da su, muna fatan rahama ga wadanda suka mutu, da fatan samun sauki cikin gaggawa ga mutanen da suka jikkata,” in ji sakon na X.

A gefe guda ma China da India duk sun aika sakonsu na jajantawa ga Putin da mutanen Rasha baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here