Abba Gida-Gida ya nada dan Kwankwaso kwamishina 

0
347

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya turawa majalisar dokokin jihar sunayen mutane 4 wadanda yake son nada su a matsayin kwamishinoni a kunshin gwamnatinsa ciki harda da dan Kwankwaso.

Shugaban Majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya karanta sunayen a zauren majalisar a yau talata.

Gwamnan ya bukaci majalisar ta tantance tare da amince masa ya nada wadanda sukai musu Sunayen domin ya nada su a matsayin kwamishinoni.

Ga Sunayen Wadanda za’a nada din kamar haka;

1. Mustapha Rabi’u Kwankwaso

2. Adamu Aliyu Kibiya

3. Usman Shehu Aliyu Karaye

4. Abduljabbar Garko

Mustapha Rabi’u Kwankwaso dai da ne ga jagoran Kwankwasiyya kuma ubangida gwamnan Kano wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Shi kuma Adamu Aliyu Kibiya shi ne tsohon kwamishinan kasa da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar lokacin da ake shari’ar zaɓen gwamnan jihar kano, sakamakon wasu kalamai da yayi kan alƙalai.

A Kwanakin bayan gwamnan ya bada umarni ga kwamishinoninsa da su cike wani fom domin gano masu kwazo da marasa kwazo cikin Kwamishinonin, inda yayi alkawarin chanza duk kwamishinan da bai yi kwazo ba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here