Kotu ta yankewa makashin Ummita hukuncin rataya 

0
140

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa ɗanƙasar China Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe budurwarsa, Ummukhulsum Sani Buhari.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Haruna Dederi ne ya tabbatar wa yan jarida hukuncin kotun bayan zaman shari’ar da aka yi ranar Talata.

Ya ce “alƙali ya yi hukunci inda ya sami Frank da laifin kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne kuma ya zartar da hukunci a kan haka.” in ji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa “ita shari’a tana da farko tana da ƙarshe, kuma abubuwan da aka iya bi sawu aka gano yayin tuhumar wanda ake tuhuma sune ake kafa hujja da su a kai ga hukunci,”

“Abubuwan da suka gabata sune suka wajabta wa kotu ta ɗauki irin wannan matsayi.” kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

A ranar 16 ga Satumban 2022 ne ɗanChinan ya daɓa wa marigayiyar wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here