Gwamnati tayi sammacin Sheikh Gumi saboda kalamansa kan ƴan bindiga

0
183

Hukumomin tsaro sun gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi saboda kalamansa da kuma kiran da ya yi na a yi wa ƴan bindiga afuwa, kamar yadda rahotanni daga kafofin yaɗa labaran ƙasar suka nuna.

Sheikh Ahmad Gumi, wani tsohon jami’in soja ne da ke Kaduna a arewacin Najeriya kuma ya sha tayin shiga tsakanin hukumomi da kuma ƴan bindiga masu garkuwa da satar mutane don neman kuɗin fansa a ƙasar.

A baya-bayan nan ne aka ba da rahoton cewa malamin ya yi tayin tattaunawa da ƴan bindigar a kan sakin gomman ɗaliban da aka sace a farkon watan nan daga wata makaranta da ke Kuriga a jihar Kaduna.

Sai dai gwamnan Kaduna Uba Sani ya ce babu hannun Sheikh Gumi a sakin ɗaliban.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris a ranar Litinin ya ce jami’an tsaro sun gayyaci Sheikh Gumi domin yi masa tambayoyi inda ya ce malamin bai fi ƙarfin doka ba.

“Idan ka furta kalamai, musamman waɗanda suka shafi tsaron ƙasa, ya zama dole jami’an tsaro su ƙara tunani, kuma abin da suke yi ke nan,” kamar yadda aka ruwaito ministan na cewa.

A baya dai Sheikh Gumi ya yi iƙirarin ganawa da jagororin ƴan fashin daji domin neman su tuba daga sace-sacen mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here