Yan bindiga basu da banbanci da yan ta’adda – Tinubu

0
108

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bayyana cewa ya zama dole a riƙa ɗaukan mutanen da ke da hannu a aikata miyagun laifuka a matsayin ƴan ta’adda.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Talata a taron buɗe-baki tare da ma’aikatan shari’a na gwamnatin tarayya bisa jagorancin alƙalin alƙalai na ƙasa, mai shari’a Olukayode Ariwoola.

Da yake nanata ƙudirin gwamnati na murƙushe ƴan bindiga, shugaba Tinubu ya ce waɗanda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.

“Dole ne mu ayyana masu garkuwa a matsayin ƴan ta’adda,” in ji shugaban ƙasar, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ta ruwaito.

Najeriya dai tana fama da ƙaruwar matsalolin tsaro. Yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas sun yi fama da ƙaruwar sace-sacen mutane da hare-haren ƴan bindiga a shekaru 10 da suka gabata.

Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa ba za ta tattauna da ƴan bindiga ba duk da yadda suka mayar da sace mutane don kuɗin fansa a matsayin wata hanyar samun kuɗi inda suke garkuwa da ɗalibai da jama’a – hari na baya-bayan nan shi ne sace ɗalibai 137 daga Kuriga a jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here