NNPC ya karyata rade-radin rage farashin man fetur

0
191
man fetur
man fetur

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa na rage farashin man fetur daga naira 568 zuwa 560 duk lita ɗaya.

NNPCL ya ƙaryata rahotannin cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin sa Femi Soneye.

Sanarwar ta bayyana cewa NNPCL a shirye yake ya ci gaba da samar da albarkatun man da zai wadata ƙasar a dukkan gidajen mansa da ke faɗin ƙasar.

A ranar 9 ga watan Fabarairu ne NNPCL ya ce ba za a ƙara kuɗin mai ba a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here