EFCC ta cafke Bobrisky kan zargin wulakanta naira

0
137

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa ta kama, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky saboda zargin sa da wulaƙanta takardar naira.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa an kama Bobrisky ne ranar Laraba da daddare a jihar Legas.

“An tsare shi a ofishinmu na Legas kuma za a gurfanar da Bobrisky a gaban kotu.” in ji jami’in.

Ya ce “muna aiki tuƙuru wajen farfaɗo da martabar naira.

Duk da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, amma za a kai Bobrisky kotu ba da daɗewa ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here