Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci a Najeriya da su zo a haɗa kai domin a kawo ci gaba mai ɗorewa a ƙasar nan.
Shugaba Tinubu, ya yi wannan kira ne a yammacin ranar Alhamis yayin wani buɗa-baki da ya shirya wa wasu ’yan kasuwar Najeriya a fadarsa da ke Abuja.
Ya ce, bashi da dalilin kasa kawo ci gaba a Najeriya, domin shi ya riƙa yawo yana neman shugabancin Najeriya, don haka babu wani dalili da zai sa yanzu ya ce ya kasa.
“Na so a ce na gana da ku tun kafin yau, saboda kuna da matuƙar muhimmanci a tafiyar gwamnatina.
“Babu wani ɓangare a tattalin arziƙi da ya wuce ɓangaren kasuwanci, idan babu ci gaba a harkokin kasuwanci, tabbas babu ci gaba a kowane ɓangare, babu makoma mai kyau, babu wadata kuma babu maganar aikin yi, duk yadda za a yi, in dai harkokin kamfanoni masu zaman kansu ba ya ci gaba, to labari ne kawai, babu abin da za a aikata.”
Ya kara da cewar, “Na gode da juriyar da kuke nunawa. Muna wata gaɓa mai tsauri na kawo sauyi mai ɗorewa a bangaren tattalin arziƙinmu.
“Ba sai na yi muku gwari-gwari ba. Ina so na gode muku bisa jajircewarku, duk da yadda abubuwa suka yi tsauri,” in ji Tinubu.
Tinubu ya ce a lokacin da ya je ziyarar aiki birnin New York na ƙasar Amurka, yayin taron hada-hadar hannun jari a 2023 ya bayyana wa mahalarta taron cewae su ɗauki Najeriya a matsayin babbar ƙasa.
“Na faɗa musu su ɗauki Najeriya a matsayin babbar ƙasar zuba jari.
“A karshen jawabina, na sanar da su muna son su zo ne domin haɓaka tattalin arziƙin Najeriya, ba wai don ba za mu iya yi da kanmu ba, sai domin bayar da dama ga duk mai buƙata.”
A nasa jawabin, Mista Tony Elumelu, shugaban kamfanin Heirs Holdings, ya tabbatar wa shugaban kasar cewa kungiyar yan kasuwa masu zaman kansu (OPS) a kasar nan suna tare dashi kima za su cigaba da mara masa baya.
Toni ya ce ”Shirin gwamnatinka na sauya fasalin tattalin arziki da kasuwanci a Najeriya ya dace”.
“Muna yabawa da abin da kuke yi. Mun san ana jin jiki, amma idan muka jure za mu yi nasara”
Ya ci gaba da cewa “Mun yaba da shawarwarinku, kuma mun jinjina wa da abin da kuke yi. Kun kun nunawa duniya cewa kuna da sha’awar ci-gaban Najeriya”.
“A madadin sauran ‘yan kasuwa masu zaman kansu, muna so mu tabbatar muka cewa muna tare da gwamnatin ka dari bisa dari. Muna magana da ministocinka lokaci bayan lokaci”.