An soma shari’ar Binance da gwamnatin Najeriya kan haraji

0
100

Shari’ar kin biyan haraji da ta shafi hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC da dandalin musayar kudaden intanet, Binance da shugabanninta guda biyu ta sami tsaiko, a ranar Alhamis.

Wannan ya biyo bayan gazawar hukumar haraji ta Najeriya, FIRS, ta yi na bayyana tuhuma-tuhuman da ake yi wa waɗanda ake zargi.

A babbar kotun tarayya da ke Abuja, daya daga cikin shugabannin Binance Tigran Gambaryan ne kawai ya gurfana a gaban mai shari’a Emeka Nwite, yayin da Nadeem Anjarwalla ba ya nan, inda har ya zuwa yanzu ba a san inda yake ba, bayan ya tsere daga tsarewar da aka yi masa bisa wasu sharudda da ba a tabbatar ba.

Lauyan Gambaryan ya shaida wa kotun cewa ba za a iya gurfanar da wanda yake karewa ba saboda ba a gurfanar da shi a tuhumar FIRS ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa lauyan Gambaryan ya shaida wa kotu cewa ba za a iya gurfanar da wanda yake karewa ba saboda ba a tuhume shi da laifin komai ba.

Daga bisani alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Afrilu.

A watan da ya gabata ne dai, hukumar tattara harajin cikin gida ta ƙasar ta shigar da tuhumar kin biyan haraji a kan dandalin Binance kuma ta sanya sunan Anjarwalla da Gambaryan a cikin wadanda suka amsa.

A ranar Laraba ne Binance ya fitar da wata sanarwa inda ta buƙaci a saki Tigran Gambaryan wanda suka ce a baya ya hada kai da hukumomin Najeriya wajen yaki da miyagun laifuka da garkuwa da mutane da kuma kwace kadarorin da suka kai kimanin dala 400,000.

A halin da ake ciki, hukumomin Najeriya sun ce suna aiki tare da ƴan sandan ƙasa da ƙasa domin bayar da sammacin ƙasashen duniya na kama Mista Anjarwalla.

Hukumar harajin Najeriya ta zargi Binance da ƙin biyan harajin da ake sawa kan kayayyaki da harajin samun kuɗin shiga na kamfani da gazawar shigar da bayanan haraji, da kuma haɗa kai wajen taimaka wa abokan ciniki su guje wa haraji ta hanyar Binance.

Babban bankin Najeriya ya kuma bayyana cewa kusan dala biliyan 26 ne aka yi hada-hadar kasuwanci a Binance Nigeria tare da wasu majiyoyi da ba a gano su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here