Wakilan Isra’ila da Hamas sun sake haduwa a birnin Alkahira kan tsagaita wuta

0
151

An ci gaba da tattauna wa tsakanin wakilan Isra’ila da na kungiyar Hamas a karkashin shiga tsakanin Amurka da Masar a birnin Alƙahira a karshen makon nan, don kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin mutanen da bangarorin masu rikici ke garkuwa da su.

Wannan sabon yunkuri na zuwa a yayin da ake shirin cika watanni shidda da barkewar yakin Isra’ila da Hamas a Gaza, bayan farmakin da mayakan kungiyar ta Hamas suka kai a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar bara.

Gabanin haduwar ta yau, sai da Hamas ta nanata manyan sharuddan da ta gindaya kafin kulla yarjejeniyar tsagaita wutar, da suka hada da janye baki dayan sojojin Isra’ila daga Gaza, da kuma kawo karshen kai hare-hare a ilahirin Zirin.

Alkaluman baya bayan nan da ma’aikkatar lafiyar yankin na Gaza ta fitar sun bayyana mutuwar Falasdinawa sama da dubu 33 akasarinsu mata da kananan yara, tun bayan hare-haren ramuwar neman shafe Hamas da sojojin Isra’illa suka kaddamar fiye da watanni 5 da suka gabata.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here