‘Yan bindiga sun hallaka mutane da dama a jihar Kogi

0
97

‘Yan bindiga sun kashe mutane akalla 21 a jihar Kogi da ke yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, rikicin da mahukunta suka bayyana a matsayin na manoma da makiyaya.

Shugaban karamar hukumar Omala inda lamarin ya auku Edibo Ameh Mark, ya tabbatar da binne mutanen 21 da suka rasa rayukan nasu a ranar Juma’a.

Mark ya kara da cewar farmakin da Fulani makiyayan suka kai na ramuwar gayya ne akan kashe ‘yan uwansu shidda, biyu daga cikinsu ta hanyar fille musu kai da wasu mazauna daya daga cikin kauyukan karamar hukumar ta Omala suka yi kwanaki uku kafin harin ramuwar.

Wani mazaunin yankin da ya shaida aukuwar lamarin Atabor Juluis, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ‘yan bindiga kimanin 100 ne suka afka wa yankin nasu a ranar Alhamis din da ta gabata.

A cewar Juluis gawarwakin mutane 19 suka gano jim kadan bayan harin, da safiyar ranar Juma’a kuma suka gano karin gawarwaki 15, wadanda ya ce akasarinsu tsofaffi ne ba suka gaza tserewa maharan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here