Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban watan sallah 

0
182

Kwamitin ganin wata na Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmin ƙasar su fara duban watan Shawwal a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da kwamitin ya fitar yau Lahadi a Sokoto.

“Duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi,” in ji sanarwar.

Fadar Sarkin Musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here