Yadda rikicin siyasa ya kaure tsakanin gwamnatin jihar Kano da Ganduje

0
123

A na ci gaba da ce-ce-ku-ce tsakanin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da tsohon gwamnan Kanon Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnatin Kanon ta ce maimakon Ganduje ya riƙa tsoma baki cikin salon mulkinsu,kamata ya yi ya mayar da hankali kan yadda zai kare kansa daga tuhume-tuhumen da ake masa.

Gwamman na Kano ya ce tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC a kasar na ruko Abdullahi Umar Ganduje ba shi da bakin magana kan yadda suke tafiyar da harkokinsu na gwamnati, ganin irin badakalar da ake zargin an tafka a lokacin da yake gwaman a jihar, tsawon shekara 8.

Mai Magana da Yawun gwamnan na Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce a tsawon wa’adin muklin da ya yi karo biyu gwamnatin sa cike ta ke da barnatar da dukiyoyin al’umma, kamata ya yi ya mayar da hankalinsa yadda zai kare kansa zarge zargen da ake yi masa shi da iyalansa.

Haka kuma ya ce abin kunya ne a ce gwamnan ya tunkari kafafen yada labarai ya ce zai yi wata magana ta kare kansa, duk kuwa da cewar akwai wani bidiyo da suke zargin shi ne ke karbar cin hanci da ya ce wannan ya zubar wa da al’ummar jihar Kano mutunci a idon duniya.

“Muna kira ga hukumar EFCC da ta fito da ainahin binciken da ta yi a kan wannan bidiyo na dala da ta yi tun shekarar 2018, domin al’umma su san na gaske ne ko akasin haka” cewar Sanusi Bature.

Wannan taƙaddama na zuwa ne mako daya da kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan barnatar da dukiyar al’umma da rikice-rikicen siyasa musamman na fadan daba, da gurfanar da shi da iyalinsa a gaban kotu kan zargin almundahana da dala dubu dari 413, da wata naira tiriliyan 1, da miliyan 38 a jihar a tsakanin 2015 zuwa 2023.

To sai dai bangaren tsohon gwamman na Kano Abdullahi Umar Ganduje sun mayar da martani cewar Abba Kabir Yusuf din na amfani da hakan ne don dauke hankalin al’umma daga kan gazawarsa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Edwin Olofu shi ne sakataren yada labaran Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce wannan maganganu na gwamnatin Kano duk shaci fadi ne.

“Saboda babu abin da suke yi na a zo a gani tun da suka hau mulki shi ya sa suka dauko maganar bincike domin su ci masa zarafi shi da iyalansa,”cewar Edwin.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here