Kotu ta ayyana ranar gurfanar da Ganduje a gabanta 

0
172
Gwamna Ganduje
Gwamna Ganduje

Wata babbar kotu a Kano ta saka ranar 17 ga watan Afrilu, 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, da kuma wasu mutane shida kan zargin almubazzaranci. 

Waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci na kuɗin dala, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.

A cikin takardar sammacin, sauran waɗanda ake karar sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da kuma Lesage General Enterprises.

A karar da gwamnatin jihar ta Kano ta shigar a kan waɗanda ake zargi su takwas, ta ce ta haɗa shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.

An tsayar da ranar 17 ga Afrilun domin fara sauraron shari’ar wanda mai shari’a Usman Na’aba na babbar kotun jiha mai lamba huɗu zai jagoranta.

Babban Lauyan gwamnatin jihar wanda kuma shi ne kwamishinan shari’a, Haruna Isah Dederi, ya tabbatar da cewa Ganduje, matarsa da wasu mutane shida za a gurfanar da Ganduje, matarsa da kuma wasu mutum huɗu a ranar da aka bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here