Hankali ya karkata kan martanin da Isra’ila za ta mayar wa Iran

0
149

Sojojin Isra’ila sun ce kashi 99 na hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa da Iran ta harba an daƙile su ba sukai inda aka harba su ba. 

Iran ta ce hare-haren na ramuwar gayya ne kan harin da Isra’ila ta kai wa ofishin jakadancinta da ke Syria makonni biyu baya.

Yaya wannan rikici zai kasance, hakan ya ta’allaka da yadda Isra’ila ta kalli hare-haren da Iran ta kai mata ranar Asabar da daddare.

Ƙasashen da ke yankin da sauran yankunan duniya ciki har da waɗanda ba sa son Iran na ta kiraye-kirayen a kwantar da hankali.

Matsayar Iran ita ce hatin nata ya zama ba za a rama shi ba, ma’ana matsalar ta ƙare daga nan, “ta kuma ja kunnen Isra’ila kan cewa ka da ta yi yunƙurin kai mata hari, idan ba haka ba za ta sake kai mata hari mai ƙarfi da ba za ta iya tare wa ba.”

Amma Isra’ila ta sha alwashi “mummunan hari” kuma gwamnati ta kira wannan hari mafi muni a tarihin Isra’ila na baya-bayan nan.

Idan aka dubi yadda ta mayar da martani kan harin da Hamas ta jangoranta na ranar 7 ga watan Oktoba a kudancin Isra’ila cikin gaggawa, da kuma ɗaukar watanni shida da ta yi tana luguden wuta a Gaza. 

Da yiwuwar majalisar yaƙin Isra’ila ba za ta kyale wanna harin na kai tsaye ba ya tafi ba tare da mayar da martani ba.

Za ta iya sauraren makwabtanta na yankin ta yi abin da ake kira “mai hakuri shi ke dafa dutse” ta ki mayar da martani ta irin hanyar da aka kai mata harin, maimakon haka a ci gaba da yaƙin nesa-nesa tare da ƙawayenta da ke yankin irinsu Hezbollah da ke Labanon da kuma ma’ajiyar makamanta da ke Syria, kamar dai yadda suke yi tsawon shekaru.

Isra’ila za ta iya kai harin samuwa a jere kamar yadda aka yi mata, cikin nutsuwa da kuma hare-haren makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa inda Iran ta riƙa kai mata hari daga wurin a daren jiya.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here