‘Bai dace a sake’ yin wani yaki a Gabas ta Tsakiya da duniya ba – MDD

0
167
MDD

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargaɗi ga ƙasashen duniya ranar Lahadi game da faɗawa cikin babban rikici, inda ya gabatar da jawabi ga Kwamitin Tsaron na Majalisar kan harin da Iran ta kai wa Isra’ila a ƙarshen mako.

“Bai dace yankin (Gabas ta Tsakiya) da ma duniya su sake tsunduma cikin wani yaƙi ba,” in ji Guterres.

“Gabas ta Tsakiya yana cikin yiwuwar faɗawa cikin bala’i,” kamar yadda ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

“Al’ummar wannan yanki na fuskantar babban hatsari na shiga cikin yaƙi tsundum. Lokaci ya yi da za a kai zuciya nesa,” in ji shi, yana mai cire da a yi “matukar taka-tsantsan.”

Ranar Asabar da ta gabata, Iran ta ƙaddamar da hari kai-tsaye a cikin Isra’ila a karon farko, inda ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 300.

Isra’ila da ƙawayenta, waɗanda suka haɗa da Amurka, Jordan da Birtaniya sun kakkaɓo kusan dukkansu.

Rundunar sojojin Isra’ila ta ce mutum 12 sun jikkata sakamakon harin.

Iran ta ce ta kai harin ne domin yin ramuwar gayya bisa harin da aka kai ƙaramin ofishin jakadancinta da Damascu ranar 1 ga watan Afrilu, wanda ta ɗora alhakin kai si a kan Isra’ila.

Harin ya kashe zaratan sojoji bakwai na runduna ta musamman ta Iran, wato Revolutionary Guards, cikinsu har da janar-janar guda biyu, lamarin da ya hasala Iran wadda ta sha alwashin yin raddi.

Wannan tata-ɓurza ta haddasa ƙarin fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya game da yiwuwar ɓarkewar sabon yaƙi, ciki har da yiwuwar martani daga Isra’ila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here