Yan bindiga sun saki ragowar daliban jami’ar Gusau 

0
153

Ƴan uwa da iyayen ɗaliban jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara da aka yi garkuwa da su sun tabbatar da sakin ragowar ɗaliban da suka rage a hannun ƴan bindiga. 

Sun ce tun a ranar Juma’ar da ta gabata aka saki rukuni na farko kafin daga bisani a sako sauran da yammacin ranar Lahadi.

A watan Satumban bara ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban daga ɗakin kwanansu da ke wajen jami’ar. 

Yar uwar wani mutum da ya nemi a sakaya sunansa na cikin ɗaliban da aka sako ranar Lahadi kuma ya shaida wa BBC cewa tun bayan da aka sace ɗaliban suna magana da su ta waya lokaci zuwa lokaci.

Ya ce “ranar Juma’a an saki mutum uku, da aka sako su babu ƴar uwata a ciki, ranar Lahadi kuma, wasu daga cikin yaran sai suka kira iyayensu mata suka yi magana da su cewa an karɓo su, ga su a hannun jami’ai cewa za a tafi da su Gusau.” in ji shi.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here