Dangote ya karya farashin man  dizel

0
268
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man dizel zuwa Naira dubu daya.

A lokacin da Dangote ya fara fitar da dizel din kamfaninsa ana sayar man dizel a kasuwanni Naira 1,600 zuwa Naira 1,700.

Sai ya fito da nasa a kan N1,200, nan take aka samu saukin N450 zuwa N500.

A ranar Talatar aka gano cewa farashin litar dizel din ya zama N1,000, an sake samun saukin N200.

A ziyarar Barka da Sallah da Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangotem ya kai wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a Legas, dan kasuwan ya bayyana cewa ragin da kamfaninsa ya samar zai kawo saukin farashin kayayyakin masarufi a Najeriya.

Yayin ziyarar, Dangote ya bayyana cewa sauki na tafe a Najeriya, domin kuwa kasar na kan tafarkin da ya dace.

Ya ce: “Na yi imani cewa muna kan hanya madaidaiciya. Gaskiya ne ’yan Najeriya sun yi hakuri kuma ina da yakinin cewa abubuwa da yawa za su yi sauki yanzu.

“Akwai cigaba da yawa domin idan ka duba, daya daga cikin manyan matsalolin da muka samu shi ne faduwar darajar Naira, Dala ta yi tashin gwauron zabo zuwa kusan N1,900.

“Amma a yanzu, Dala ta dawo kusan N1,300, wanda hakan nasara ce.

“Farashin kayayyaki da yawa sun haura. Idan ka je kasuwa, alal misali, wani abu da muke samarwa a gida kamar gari, shi ma ya daga.

“Me yasa? Saboda suna sayen man dizal da tsada sosai.

“Yanzu a matatar manmu, mun fara sayar da man dizail a kan  N1,200 maimakon N1,650 kuma na tabbata idan muka ci gaba da tafiya abubuwa za su kara inganta sosai.

“Idan ka kwatanta da  lokacin da ake sayen litar dizel N1,650 ko N1,700 wannan saukin da muka samar zai taimaka wurin kawo saukin farashin kayayyaki.

“Na tabbata idan alkaluman hauhawar farashin kayayyaki suka fito a wata mai zuwa, za ku ga cewa an samu sauki sosai a farashin kayayyaki.”

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here