Gwamnatin Nasarawa ta haramta kungiyoyin yan sa-kai na kabilu

0
96

Gwamnatin jihar Nasarawa ta haramta ayyukan ƙungiyoyin ƴan sa-kai na kabilu da ke aiki a faɗin kananan hukumomi 13 da ke jihar. 

Hakan ya biyo bayan wani taron gaggawa ne da gwamna Abdullahi Sule ya jagoranta.

Haka-zalika gwamnatin jihar ta ba da wa’adin makonni biyu ga ɗukkan ƙungiyoyin ƴan sai kai da umarnin ya shafa da su miƙa kayan sarki, wato inifam da kuma makamansu ga kwamishinan ‘yan sandan jihar.

kwamishinan Shari’a na jihar ta Nasarawa, Barrister Magaji Labaran, ya faɗa wa BBC cewa an ɗauki matakin ne saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu yankuna na jihar. 

“Cikin abubuwan da suka sa aka haramta ƙungiyoyin ƴan sa kai shi ne ganin cewa duk wata kabila idan ta tashi sai ta kirkiro da ƴan sa kai. An yi duba an ga cewa waɗannan ƙungiyoyi za su kawo barazana ga zaman lafiya a jihar,” in ji shi. 

Ya ce duk wata ƙungiya ta ƴan sa kai da za a kafa nan gaba, ya kasance ba ta da ɗauki wani ɓangare guda ba.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here