APC za ta ci gaba da zaben fitar da gwanin gwamnan Ondo a yau Lahadi

0
179

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fitar da gwanin gwamnan jihar Ondo na jam’iyyar APC, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Kogi Alhaji Usman Ododo ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da gudanar da zaɓen fitar da gwanin a ƙaramar hukumar Okitipupa a yau Lahadi.

A ranar Asabar ne dai jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin gwamnan a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ya ce ya samu rahoton gudanar da zaɓen fitar da gwanin a mazaɓu 203 na ƙananna hukumomin jihar 18.

Sai dai gwamnan na Kogi ya ce bayan samun sahihan rahotonnin da ke nuna cewa ba a gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar Okitipupa ba, kwamitin ya ɗauki matakin gudanar da zaɓen a mazaɓu 13 na ƙaramar hukumar a yau Lahadi.

Usman Ododo ya ce za a gudanar da zaɓen a ƙaramar hukumar da tsakar ranar Lahadi, kafin a fara tattara sakamakon zaɓen.

Gwamnan ya kuma yaba da yadda aikin zaɓen fitar da gwanin ke gudana a faɗin jihar.

Hukumar zaɓen ƙasar INEC dai ta ce cikin watan Nuwamba mai zuwa ne za ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here